Matthew 17

1Bayan kwana shida Yesu ya dauki Bitrus da Yakubu, da Yahaya dan’uwansa, ya kai su kan wani dutse mai tsawo su kadai. 2Kamanninsa ya canja a gabansu. Fuskarsa ta haskaka kamar rana, kuma rigunansa suka yi kyalli fal.

3Sai ga Musa da Iliya sun bayyana garesu suna magana da shi. 4Bitrus ya amsa ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ya yi kyau da muke a wurin nan. In kana so, zan yi bukkoki uku daya dominka, daya domin Musa, daya domin Iliya.”

5Sa’adda yake cikin magana, sai, girgije mai haske ya rufe su, sai murya daga girgijen, tana cewa, “Wannan kaunattacen Dana ne, shi ne wanda yake faranta mani zuciya. Ku saurare shi.” 6Da almajiran suka ji haka, suka fadi da fuskokinsu a kasa, saboda sun tsorata. 7Sai Yesu ya zo ya taba su ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.” 8Amma da suka daga kai ba su ga kowa ba sai Yesu kadai.

9Yayin da suke saukowa daga dutsen, Yesu ya umarce su, ya ce, “Kada ku fadawa kowa wannan wahayin, sai Dan Mutum ya tashi daga matattu.” 10Almajiransa suka tambaye shi, suka ce, “Don me marubuta ke cewa lallai ne Iliya ya fara zuwa?”

11Yesu ya amsa ya ce, “Hakika, Iliya zai zo ya maido da dukan abubuwa. 12Amma ina gaya maku, Iliya ya riga ya zo, amma ba su gane shi ba. A maimakon haka, suka yi masa abin da suka ga dama. Ta irin wanan hanya, Dan Mutum kuma zai sha wuya a hannunsu. 13Sa’annan almajiransa suka fahimci cewa yana yi masu magana a kan Yahaya mai Baftisma ne.

14Da suka iso wurin taron, wani mutum ya zo gunsa, ya durkusa a gaban sa, ya ce, 15“Ubangiji, ka ji tausayin yarona, domin yana da farfadiya, kuma yana shan wuya kwarai, domin sau da yawa yana fadawa cikin wuta ko ruwa. 16Na kawo shi wurin almajiran ka, amma ba su iya su warkar da shi ba.”

17Yesu ya amsa ya ce, “Marasa bangaskiya da karkataccen zamani, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe zan jure da ku? Ku kawo shi nan a wurina.” 18Yesu ya tsauta masa, sai aljanin ya fita daga cikinsa. Yaron ya warke nan take.

19Sai almajiran suka zo wurin Yesu a asirce suka ce, “Me ya sa muka kasa fitar da shi?” 20Yesu ya ce masu, “Saboda karancin bangaskiyarku. Domin hakika, ina gaya maku, in kuna da bangaskiya ko da kamar kwayar mastad, za ku ce wa wannan dutse, ‘Matsa daga nan ka koma can,’ zai kuwa matsa kuma ba abin da zai gagare ku. 21[Irin wannan aljanin bashi fita sai tare da addu’a da azumi].

22Suna zaune a Galili, Yesu ya ce wa almajiransa, “Za a bada Dan Mutum ga hannun mutane. 23Kuma za su kashe shi, a rana ta uku zai tashi.” Sai almajiransa suka yi bakin ciki kwarai.

24Da suka iso Kafarnahum, mutane masu karbar haraji na rabin shekel suka zo wurin Bitrus suka ce, “Malaminku na ba da rabin shekel na haraji?” 25Sai ya ce, “I.” Amma da Bitrus ya shiga cikin gida, Yesu ya fara magana da shi yace, “Menene tunaninka Saminu? Sarakunan duniya, daga wurin wa suke karbar haraji ko kudin fito? Daga talakawansu ko daga wurin baki?”

26Sai Bitrus ya ce, “Daga wurin baki,” Yesu ya ce masa, “Wato an dauke wa talakawansu biya kenan. Amma don kada mu sa masu karbar harajin su yi zunubi, ka je teku, ka jefa kugiya, ka cire kifin da ya fara zuwa. Idan ka bude bakinsa, za ka sami shekel. Ka dauke shi ka ba masu karbar harajin nawa da naka.

27

Copyright information for HauULB